'Yan bindiga sun kaiwa motar fasinjoji hari sun kashe mutum daya

'Yan bindiga sun kaiwa motar fasinjoji hari sun kashe mutum daya

'Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai wa fasinjoji hari kan hanyar Ife zuwa Ibadan inda suka kashe wani mutum daya mai suna Adenipekun Ademiju, ma'aikacin a karamar hukumar Atakumosa na jihar Osun.

Mr Ademiju da sauran fasinjojin sun shiga motar ne a garin Osu inda za su tafi Ibadan amma sai 'yan bindigan suka kai musu hari a garin Ikire da hanyar zuwa Ibadan.

A cewar wani shaidan ganin ido, 'yan bindigan sun harbi Ademiju ne a lokacin da suka bude wa motar wuta don tilastawa direban ya tsaya.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Shaida ya bayyana yadda Abiola ya mutu ana daf da sakin sa

"Makiyaya da suka saba yin fashi a kan hanyar nan ne suka kashe mutumin.

"Ademiju da direban ne suke cikin motar amma lokacin da 'yan fashin ke harbi sai harsashi ya ratsa jikin marigayin.

"Direban ya tsere cikin daji ya bar gawar Ademiju yayin da su kuma 'yan fashin suka tafi da motar," inji shaidan.

Kakakin Rundunar Yan sanda na Jihar, SP Folashade Odoro ta tabbatar da afkuwar lamarin a hirar da tayi da manema labarai inda ta ce har yanzu suna gudanar da bincike.

An gano cewa 'yan fashi da masu satar mutane domin karbar kudin fansa sun dade suna kai wa fasinjoji hari a sassan kasar da dama cikin 'yan shekarun nan.

A yayin da masu fashi da makami da satar mutane ke kai hare-haren su, gwamnatin tarayya da kaddamar da shirye-shiryen tsaro domin magance ba ta garin kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel