Farawa da iyawa: Gwamnan Borno baizo da wasa ba

Farawa da iyawa: Gwamnan Borno baizo da wasa ba

-Gwamnan Borno ya bada umurni da a dakatar da malaman makaranta 42 daga aiki

-Babagana Zulum ya sha alwashin duba matsalolin tsaro, talauci da kuma ingantaccen ilimi.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya umurci a dakatar da malaman firamare 42 abisa dalilin guduwa daga fagen aiki tsawon shekara biyu a karamar hukumar Gamboru dake jihar.

Malam Umara, tsohon malamin jami'a ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ranar dimukaradiyya a filin Ramat square dake a Maiduguri.

Ya ce a lokacin da yake zagaye a karamar hukumar Gamboru Ngala, ya gano cewa akwai malaman makaranta 62 amma 11 kawai ke a wajen aiki.

“Abinda ya bani mamaki shine, da shugaban makarantar yace mani malamai 11 kawai gareshi tsawon shekara biyu.

“Wannan abune marar kyau kuma na bada umurni da a dakatar da malamai 42 da basu nan.” Inji shi

Ya ce bazai amince da dabi’ar kalula, rashin da’a da rashin biyayya a bangaren aikin gwamnati ba, inda yayi nuni da cewa tsananin kula da kudaden gwamnati, gaskiya da amana sune zasu tafiyar da ayyukan ma’aikatan gwamnati a jihar.

KARANTA WANNAN: Atiku yayi dai-dai da ya kalubalanci nasarar Buhari - Jonathan

Zulum ya kara da cewa za a sanya matakai masu kyau wajen ganin anyi aiki kamar yadde mutane ke tsammani.

“Zamu duba matsalolin tsaro, talauci, ilimi ingantacce, bangaren lafiya, gine gine da dai sauran abubuwanda da zasu inganta rayuwar mu. Wannan duk ba zai samu ba sai da shugabanci na gari.” Inji shi

A lokacin da yake maida bayani, Shugaban kungiyar malaman makaranta na jihar, Jubril Muhammad, ya ce malaman basu yi hakanan da gan gan ba.

Muhammed ya ce malaman suna aikin kama kama ne na sati biy- biyu.

“Malam farko an kaisu wuraren da aka kwato daga hannun yan ta’adda, su kuma sauran da suke canjin su duk bayan sati biyu, suna aiki ne a sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri.

“Bazaya yiyu ba ace dukkan malaman suna a waje guda, saboda matsalolin da muke fama dasu. Bamu da isassun malaman da zasu koyar a kananan hukumomi da kuma sansanonin yan gudun hijira a lokaci guda

“Haka zalika yawancin malam mu sun rasa komai nasu na rayuwa, sannan ga matsalolin masauki a kananan hukumomin” inji shi

Daga karshe, shugaban kungiyar ya roki gwamnan da yayi ma malaman afuwa.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel