Wuraren da sabuwar gwamnati na za ta mayar da hankali a kai - Buhari

Wuraren da sabuwar gwamnati na za ta mayar da hankali a kai - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin fayyace inda alkiblar sabuwar gwamnatin sa za ta fuskanta a wa'adi na biyu, ya sake jaddada aniyar sa ta bunkasa tattalin arziki da kuma tsarkake kasar nan daga annobar ta'addanci.

Cikin jawaban da ya gabata yayin bikin ranar dimokuradiyya da aka gudanar cikin garin Abuja a ranar Laraba 12, ga watan Yunin 2019, shugaba Buhari ya ce aukuwar miyagun ababe na ta'addanci ta kai intaha da gwamnatin sa za ta ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen ta.

Yayin bikin da aka gudanar a dandalin Eagle Square dake babban birnin kasar nan na Tarayya, shugaba Buhari ya zayyana wasu daga cikin manufofin sabuwar gwamnatinsa da suka hadar da inganta manyan makarantu wajen assasa cibiyoyin bincike na fasahar zamani.

Domin sanya Najeriya a sahu na gaba tare da goga kafadar ta da sauran kasashe da suka taka mataki na ci gaba, Buhari ya ce gwamnatin sa za ta jajirce wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya wajen horar da ma'aikatan lafiya tare da samar da kayan aiki na zamani.

Dangane da bunkasa harkokin noma, Buhari ya ce al'ummar Najeriya su sha kurumin su domin kuwa sabuwar gwamnatin sa za ta zage dantsen ta wajen bayar da kyakkyawan tallafi musamman ga manoman shinkafa, masara, rogo, kaji, taki da kuma iri na zamani wajen ganin kasashen duniya sun kwadaita da amfanin gona na kasar nan.

KARANTA KUMA: Hanyoyi 8 da Buhari zai yaki rashawa a wa'adi na biyu

Bayan gargadin masu yiwa tattalin arzikin kasar nan ta'annati, a karshe shugaban kasa Buhari ya kuma sha alwashin inganta ci gaban ginin kasa wajen samar da gine-gine na zamani musamman na harkar sufuri da kuma kiwon lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel