Osinbajo ya karbi bakuncin tawagar wakilan kasar Indiya a fadar Villa

Osinbajo ya karbi bakuncin tawagar wakilan kasar Indiya a fadar Villa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin Tarayyar Najeriya da kumata kasar Indiya za su ci gaba da kasancewa aminan juna da habaka dangartakar dake tsakanin su musamman a fannin bunkasa tattalin arziki.

Furucin Farfesa Osinbajo ya zo ne a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin karbar bakuncin tawagar gwamnatin kasar Indiya bisa jagorancin Ministan harkokin kasashen ketare, Mista V. Muraleedharan.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban Mista Laoulu Akande ya bayyana cewa, wakilan na kasar Indiya na cikin manyan baki da suka halarci bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya da aka gudanar a ranar Laraba a dandalin Eagle Square dake garin Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya ce ya kamata Najeriya ta yi da kasar Indiya musamman a bangaren bunkasar ci gaban da ta samu cikin tsawon shekaru kimanin goma da suka shude duk da yawan al'ummar ta.

Legit.ng ta ruwaito, yau Laraba 12, ga watan Yunin 2019, aka gudanar da bikin sabuwar ranar dimokuradiyyar kasar nan bayan da shugaban kasa Buhari ya lamucewa sauya ranar daga 29 ga watan Mayu kamar yadda aka saba a baya.

KARANTA KUMA: Wuraren da sabuwar gwamnati na za ta mayar da hankali a kai - Buhari

Shugaban kasa Buhari cikin jawaban da ya gabatar bayan fayyace sabbin hanyoyin yaki da rashawa, ya kuma zayyana sabbin akidu da sabuwar gwamnatin sa a wa'adi na biyu za ta mayar da hankali a kai domin fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel