Yanzu Yanzu: Jirgin yakin soji ya yi saukar gaggawa a hanyarsa ta dawowa daga Katsina

Yanzu Yanzu: Jirgin yakin soji ya yi saukar gaggawa a hanyarsa ta dawowa daga Katsina

Wani jirgin yakin soji ya yi saukar gaggawa a hanyarsa ta dawowa daga aikin kakkabe yan ta’adda wanda ke gudana a yankin arewa maso yamma a karkashin shirin Operation Hadaran Daji.

Zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan afkuwar hatsarin wanda ya faru a jihar Katsina a yau Laraba, 12 ga watan Yuni.

Sai dai kuma an tattaro cewa ba a rasa rai ban a mutanen da ke cikin jirgin da kuma wadanda ke kasa a lokacin da abun ya afku.

Shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar, ya umurci sashin bincike na hukumar da tayi gaggawan bincike domi gano ainahin abunda ya haddasa afkuwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari yayi magana kan wadanda ke daukar nauyin rashin tsaro a Najeriya

Hukumar ta bayyana cewa a kullun tana neman fahimta da tallafin jama’a yayinda take kan jajircewa a kullun domin ganin ta tsare Najeriya da yan Najeriya baki daya.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton 'yan bindigan ne sun sace sarkin garin Labo da ke karamar hukumar Batsari na Jihar Katsina a ranar Talata.

A halin yanzu ba a bayyana sunan sarkin kauyen ba da aka ce an sace shi misalin karfe 1 na rana a gonarsa tare da wasu mazauna kauyen kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wasu da suka bayyana abinda ya faru sun ce 'yan bindigan sun kai farmaki gonakin a kan babura suna harbe-harbe kuma cikin wannan hargitsin ne aka sace sarkin kauyen yayin da wasu da ke tare da shi suka tsere.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel