Yanzu Yanzu: Buhari yayi magana kan wadanda ke daukar nauyin rashin tsaro a Najeriya

Yanzu Yanzu: Buhari yayi magana kan wadanda ke daukar nauyin rashin tsaro a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mafi akasarin rikicin kabilanci da na addinai da ke faruwa shugabannin kabila, siyasa ko na addini ne ke daukar nauyinsu da rura wutarsu.

Shugaban kasar wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a bikin ranar Damokradiyya a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni a Abuja, ya bayyana cewa shugabannin na burin cimma burinsu ta hanyar “amfani da rabuwar kawunanmu da kura-kurai, inda hakan ke dada raunana kasarmu”.

Ya bayyana cewa duk da ayyukan masu barna da gangan, gwamnatinsa na ci gaba da mayar da hankali wajen cika alkawaran zaben da ta dauka a fannin tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Shugaban kasar ya sake jadadda girman ajeriya a tsakanin kasashe da kuma bukatar dukkanin yan kasa suyi aiki a tare wajen ganin an dawo da martabarta.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci zuwa ga tafarkin ci gaba a shekaru 10 masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 8 da Buhari zai yaki rashawa a wa'adi na biyu

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin bude taro a wajen bikin ranar 12 ga watan Yuni, wacce ta kasance ranar bikin Damokradiyya a Abuja.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da bunkasa tattalin arziki domin fitar da Najeriya daga talauci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel