'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun yi awon gaba da wata mai jego

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun yi awon gaba da wata mai jego

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan al'ummar unguwar Rigasa dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna tare da yin awon gaba da wata mata da ke jego.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewar 'yan bindigar sun shiga gida-gida tare da yin awon gaba da mutane a harin da suka kai da misalin karfe 2:00 na dare.

Majiyar jaridar ta shaida mata cewar 'yan bindigar sun yi awon gaba da wasu 'yan mata uku amma rundunar 'yan sanda ta ce ta kubutar da duk wadanda aka sace in banda Maijegon.

Mijin matar mai suna Ibrahim ya ce 'yan bindigar sun tafi bar jaririn amma kuma sun yi awon gaba da mahaifiyarsa.

"Jaririn tare da ragowar 'ya'ya na suna makwabta, amma har yanzu matata na tare da 'yan bindigar," a cewar sa.

Ya bayyana cewar ya tsira daga sharrin 'yan bindigar ne saboda ya gudu bayan ya ji harbin bindiga a kofar gidansa da tsakar daren ranar.

Kazalika wata matashiya da ta ce sunanta Fatima ta bayyana yadda ta kubuta daga fada wa tarkon 'yan bindigar.

DUBA WANNAN: Buhari ya sabbin salo uku da gwamnatinsa ke amfani da su wajen yaki da ta'addanci

"Sun shigo gidanmu sun karbe wayar 'yar uwa ta, sannan suka umarce ni da na biyo su. Sun tambaye ni ko za a samu kudi a wuri na amma sai na ce musa bani da kudi. Haka na cigaba da kuka ina rokonsu su sake ni, saboda kukan da nake yi har sai da wani daga cikinsu ya mare ni.

"Ana cikin haka ne sai 'yan sanda suka zo, da naga sun fara musayar wuta sai na ruga da gudu na shige gida," a cewar matashiyar.

Wani mazaunin unguwar ya ce 'yan bindigar sun dauki N45,000 da suka shiga nemansa a gidansa, shi kuma lokacin ba ya gari.

"Sun shiga gida na suna nema na, a garin binciken ko na buya a wani wurin ne suka ci karo da kudi na N45,000," a cewar sa.

Yakubu Sabo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mutum daya ne 'yan bindigar suka sace, kuma tuni rundunar 'yan sanda ta tura jami'anta domin kubutar da matar da kuma kama masu laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel