Buhari ya fadi sabbin salon da gwamnatinsa ke amfani da su wajen yaki da ta'addanci

Buhari ya fadi sabbin salon da gwamnatinsa ke amfani da su wajen yaki da ta'addanci

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa na tunkarar matsalolin tsaro ta hanyar amfani da hikima, makamai da kuma naci.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gabatar da jawabi a wurin taron tuna wa da ranar Dimokraddiya, 12 Yuni, da aka yi a Abuja, ya ce babu zaman lafiya a kusan dukkan sassan kasar nan lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015.

Ya ce: "bayan karbe iko a kananan hukumomi 18 a yankin arewa ta gabas, Boko Haram na kai hari ko ina, har da Abuja.

"Kungiyar na cin karen ta babu babbaka ta hanyar kai harin bama-bamai har Ofishin majalisar dinkin duniya da hedikwatar rundunar 'yan sanda da ke Abuja.

"Na san cewar har yanzu na san kalubalen tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da aiyukan 'yan ta'adda a wasu kauyuka.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya fadi wurin da gwamnatin Buhari zata kai Najeriya

"Babban banbancin da ke tsakanin 2015 da yanzu shine muna bawa rundunonin tsaro goyon baya ta fuskar samar da kudade da kayan aiki da kuma samar da bayanan sirri gare su.

"Muna tunkarar matsalolin tsaro da hikimomi masu tasiri, amfani da makamai da kuma nacin cigaba da yaki da 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci," a cewar shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel