Hanyoyi 8 da Buhari zai yaki rashawa a wa'adi na biyu

Hanyoyi 8 da Buhari zai yaki rashawa a wa'adi na biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 11, ga watan Yunin 2019, ya shimfida wasu manyan tsare tsare takwas da zai ba muhimmancin gaske wajen yaki da rashawa a wa'adin gwamnatin sa na biyu.

Cikon jawaban da ya gabatar yayin taron yaki da rashawa na ranar dimokuradiyya da aka gudanar a garin Abuja, shugaban kasar ya ce gwamnatin sa za ta kawo wasu sabbin tsare tsare wajen tabbatar da cin nasarar fatattakar annobar rashawa daga kasar nan.

A yayin taron da hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta dauki nauyi, shugaban kasa Buhari tare da takwaransa na kasar Rwanda, Paul Kagame, sun gabatar da jawabai musamman a kan yadda za a kawo karshen annobar rashawa a nahiyyar Afirka baki daya.

Hanyoyi takwas da shugaban Buhari ya kudirci tabbatar da su a sabuwar gwamnatin sa wajen zage dantsen sa a fagen yaki da rashawa sun hadar da:

1. Inganta harkokin gudanarwa da kuma jin dadin hukumar EFCC da dukkanin hukumomi masu yakar cin hanci da rashawa a kasar nan.

2. Dakile duk wata kafa ta almundaha a majalisun Tarayya tare da tabbatar da hadin gwiwa a tsakanin bangarori uku na gwamnatin kasar nan.

3. Tabbatar da bayyana kadarorin da masu rike da madafan iko a kasar nan suka mallaka gami da dabbaka dokar hukunci a kan duk wata cibiya mai zaman kanta ko kuma ma'aikatan gwamnati da aka kama da laifin rashawa.

4. Bayar da ingatacciyar kariya ga masu fallasa wadanda suka aikata laifukan rashawa ko kuma yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

5. Kawo sabon salo na kunyatar wa da kuma bayyana sunaye karara na wadanda aka kama da laifukan rashawa tare da daga martabar wadanda suka tsarkaka daga wannan ta'ada.

KARANTA KUMA: Gwamnonin APC sun bukaci ganawa da Sanata Lawan, Gbajabiamila

6. Bunkasa hanyoyin wayar da kawunan al'ummar Najeriya a kan illolin rashawa tare da fadakar wa a kan yadda za su yaki annobar rashawa gwargwadon mataki da kuma iko.

7. Tsananta bincike tare da shimfida tsauraran mataikai wajen bankado almundahana da wawuson dukiyar kasa a nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare. Yaye shamakin sirri dake tsakanin bankuna wajen bankado masu kauracewa biyan haraji.

8. Neman hadin gwiwar kasashen duniya tare da tabbatar da sabon tsari da ya tsarkaka daga wani sharadi wajen karbo dukiyar kasar nan da aka dankare ta a wasu kasashen katare.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel