Yaki da Barayin da Buhari ya ke yi a Najeriya duk bula ce – Inji Frank

Yaki da Barayin da Buhari ya ke yi a Najeriya duk bula ce – Inji Frank

Fitaccen rikakken ‘dan gwagwarmayar nan kuma tsohon jigon jam’iyyar APC mai mulki, Timi Frank, ya bayyana cewa ba da gaske shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yakar barayin kasar ba.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust a Ranar Laraba, 12 ga Watan Yuni, 2019, Timi Frank, ya ce shugaba Buhari bai dace ya fito ya na cewa yana yakar marasa gaskiya ba.

A cewar tsohon Sakataren yada labaran na APC na kasa, kusan duk ma’aikatun gwamnatin Najeriya sun tabarbare da barna da dukiyar kasa a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Frank ya ke cewa gwamnatin Najeriya ta na yaudarar Duniya ne da cewa ta na fada da masu satar dukiyar al’umma. Frank ya ce jami’an gwamnatin APC sun fi kowa wawurar kudin Talakawa.

KU KARANTA: Nan gaba kadan El-Rufai zai fito ya soki manyan APC - Shehu Sani

Wannan Bawan Allah ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar yana mai martani ga kalaman da shugaba Buhari ya yi wajen wani taro da EFCC ta shirya a cikin makon nan a Garin Abuja.

Kamar yadda rahoto ya zo mana, Frank ya nemi shugaba Buhari ya koyi yadda ake yakar Barayi a wajen shugaban kasar Tanzaniya wanda ya zo Najeriya domin halartar wannan taro na yaki da sata.

A jawabin na Timi Frank, yace: “Na kalubalanci Buhari ya yi wa Duniya bayani a kan tallafin man fetur da NNPC ta ke biya, da kuma bayani a kan wasu makudan kudi da aka samu kwanaki a Ikoyi.”

Har wa yau, Frank ya zargi gwamnatin Buhari da yi wa Danjuma Goje afuwa saboda burin siyasa. Kwamred Frank ya ke cewa: “An kuma yi amfani da tsarin Trader-Moni wajen sayen kuri’u a zaben 2019”.

Kwamred Frank ya cigaba da cewa:

“Rashin gaskiya ne a ce ana ganin wadanda ya kamata a ce su na gidan yari, su na yawo a gari.”

Jawabin Frank din ya kare da cewa:

“An siyasantar da yaki da barayin da ake yi a Najeriya, an koma farautar wadanda ba su tare da APC”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel