Za mu fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci nan da shekara 10 – Buhari

Za mu fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci nan da shekara 10 – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci zuwa ga tafarkin ci gaba a shekaru 10 masu zuwa.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin bude taro a wajen bikin ranar 12 ga watan Yuni, wacce ta kasance ranar bikin Damokradiyya a Abuja.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da bunkasa tattalin arziki domin fitar da Najeriya daga talauci.

“Ana sanya ran GDP na kasarmu zai tashi da kaso 2.7 cikin dari a wannan shekarar.

“Wannan gwamnatin ta dauki matakan sauya kasarmu sannan ta fitar da mutanenmu daga kangin talauci.

“Da fari za mu dauki matakan hade tattalin arzikin arzikin kakkara da na kasa ta hanyar habbaka alaka da manoman kakkara da kuma kananan sana’o’i da kuma bude hanyoyi da dama.

KU KARANTA KUMA: Bai isa ace ka kaddamar da 12 ga watan Yuni ranar Damokradiyya ba – Atiku ya caccaki Buhari kan rashin mutunta doka

“Abu na biyu, dukkanin masu kananan sana’o’i a birane da garuruwa za su yi amfani da wuraren da muke dasu a yanzu domin mu ci gaba da basu karfin gwiwa da tallafi wajen samar da kayyayakin cikin gida don inganta rayuwarmu,” inji shi.

Shugaban kasar ya kara da cewa shekaru hudu da gwamnatinsa za ta yi a nan gaba zai ci gaba da inganta rayuwar mutane ta hanyar kokarin magance lamura da dama.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel