Shugaban APC a Zamfara ya dau alkawarin mara wa Gwamna Matawalle na PDP baya

Shugaban APC a Zamfara ya dau alkawarin mara wa Gwamna Matawalle na PDP baya

Shugaban jam’iyyar All Progressives Party (APC) a Zamfara, Alh. Ahmed Sani ya dauki alkawarin mara wa gwamnatin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar baya.

Sanata Ahmed Sani, wanda ya kasance tsohon sanata mai wakiltan yanki Zamfara ta yamma, ya bayar da tbbacin ne a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar, Alh. Bello Matawalle a gidan gwamnati, Gusau.

Yace: “Babu shakka, kasancewarka a matsayin gwamnan jihar Zamfara na biya nufi ne na Allah sannan duk wanda yayi yunkurin kalubalantar wannan matsaya toh bai da imani da Allah wanda kee bayar da mulki ga wanda ya so sannan ya karba a hannun wanda ya so.

“Na zo nan ne a yau domin taya ka murna sannan nayi maka fatan alkhairi a sabon gwamatin jihar da kuma baka tabbacin samun goyon bayana don ci gabanka.

“Ya mai girma, ina son baka tabbacin cewa dukkanin magoya bayana za su mara maka baya sannan za su ci gaba da jan hankulan mutanen jihar domin baka cikakke goyon bayansu da kuma wannan gwamnati musamman da shawarwari masu kyau da zai kawo ci gaban jihar,” inji sanatan.

KU KARANTA KUMA: Burina shine hada kan Najeriya- jawabin Buhari a ranar damokradiyya

Sani wanda ya kasance gwamnan farar hula na farko a jihar, ya kuma sha alwashin tallafa wa gwamnatin PDP a jihar wajen yaki da miyagun laiuka da kuma habbaka fannin lafiya da ilimi.

Da yake martani, Matawalle yayi godiya ga sanatan akan goyon bayansa, sannan ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki da dukkanin al’umma a kokarin kawo ci gaba a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel