Gwamnonin APC sun bukaci zama na musamman da Sanata Lawan, Gbajabiamila

Gwamnonin APC sun bukaci zama na musamman da Sanata Lawan, Gbajabiamila

A yayin mika sakon su na taya murna, gwamnonin jam'iyyar APC karkashin kungiyar PGF (Progressive Governors Forum), sun bukaci a basu damar gudanar da wani zama na musamman da sababbin shugabannin majalisun Tarayya.

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma ya kasance gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, shi ne ya shimfida wannan bukata cikin wata rubutacciyar wasika ta neman samun aiwatar da zama na musamman tare da sabbin shugabannin majalisu biyu na Tarayya.

Wasikar gwamna Bagudu ta shigar da wannan bukata domin samun damar gudanar da zama da shugabannin biyu wajen kulla alaka da kuma kyakkyawar dangartaka ta ina za su dosa daidai da tsare tsare na jam'iyyar APC wajen tabbatar da ci gaban kasar nan.

Bayan kaddamar da sabuwar majalisar Tarayya karo na tara a Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya kasance shugaban majalisar Dattawan kasar nan yayin da Honarabul Femi Gbajabiamila ya zamto sabon Kakakin majalisar Wakilai yayin zaben shugabannin majalisa da aka gudanar a ranar Talata.

KARANTA KUMA: Okorocha ya yiwa INEC godiyar bashi takardar shaidar cin zabe

Cikin wani rahoton mai nasaba da wanna, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnonin jam'iyyar APC sun mamaye zauren majalisar Tarayya yayin rantsar da sabbin mambobin ta da aka gudanar a garin Abuja.

Mashahurai cikin tawagar gwamnonin da suka mamaye majalisar sun hadar da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, gwamna Simon Bako Lalung na jihar Filato, gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da sauran su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel