Zaben Majalisa: Manyan Sanatoci sun tofa albarkacin bakin su

Zaben Majalisa: Manyan Sanatoci sun tofa albarkacin bakin su

Ana cigaba da maganganu na fatan alheri tun bayan da Sanata Ahmad Lawan da kuma Sanata Ovie Omo-Agege su ka lashe zabe a matsayin shugabannin majalisar dattawan Najeriya a farkon makon nan.

A Ranar Talata 11 ga Watan Yuni, 2019, manyan Sanatocin APC watau Ahmad Lawan and Ovie Omo-Agege su ka lashe zaben da aka yi, inda su ka doke Ali Ndume da kuma Ike Ekweremadu.

Sabon Sanatan APC, tsohon gwamna Ibrahim Shekarau ya yabawa yadda ‘yan majalisar dattawa su ka gudanar da wannan sha’ani, su ka zabi shugabannin su. Shekarau ya taya shugaban murna.

Malam Shekarau ya ke cewa: “Ina taya sabon shugaban majalisar dattawa Ahman Lawan murna.”

KU KARANTA: Siyasar Najeriya: Shugabannin Majalisar Dattawa daga 1960 zuwa yau

Takwaransa na jihar Kano, Sanata Barau Jibrin ya fito ya na murna da wannan nasara da majalisar kasar ta samu. Barau Jibrin shi ne Sanatan da ke wakiltar yankin Kano ta arewa a majalisar dattawa.

Matthew Urghoghide wanda Sanata ne mai wakiltar yankin jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa bai yi da-na-sanin marawa Ahmad Lawan baya ba, duk da cewa shi yana PDP.

Sanata Urghoghide ya bayyana cewa: “Ba za a samu wani rikici wannan karo a majalisa ba.”

Shi ma dai Sanata Clifford Ordia na jihar Edo ya fadawa Duniya cewa Ahmad Lawan ya marawa baya a wannan zabe da aka yi. Ordia ya ce: “Abin da ya rage shi ne a shiga bakin aikin majalisa.”

Tsofaffin shugaban majalisar kasar, har da Bukola Saraki wanda Ahmad Lawan ya gada, sun taya wadanda aka zaba murna. Adolphus Wabara ya nemi Sanatocin su kama aiki gadan-gadan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel