Bai isa ace ka kaddamar da 12 ga watan Yuni ranar Damokradiyya ba – Atiku ya caccaki Buhari kan rashin mutunta doka

Bai isa ace ka kaddamar da 12 ga watan Yuni ranar Damokradiyya ba – Atiku ya caccaki Buhari kan rashin mutunta doka

- Yayinda yan Najeriya ke bikin ranar Damokradiyya, Atiku Abubakar yayi kira ga dukkanin masoyan damokradiyya na gaskiya da su ci gaba da kyautata tsammani

- A cewar tsohon mataimakin Shugaban kasar, bai isa ace an kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Damokradiyya ba domin tana bukatar abunda ya fi haka

- Atiku ya caccaki gwamnatin Buhari, cewa a yanzu Najeriya ce hedkwatar tsantsar talauci a duniya

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yace ranar 12 ga watan Yuni shine ruhin fafutukar damokradiyya da Najeriya tayi kuma shine kofa a rayuwar kasar.

A wani jawabi da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, Atiku yace muhimmancin da ke tattare da bikin ranar 12 gaa watan Yuni, 1993, zaben Shugaban kasa ya kasance abun tunawa a tarihin kasar wajen zama kasa mai yanci.

Yace shekaru 26 da suka wuce, yan Najeriya sun zabi damokradiyya akan mulkin zalunci. “hukuncin da yan Najeriya suka yanke a wannan rana na zabar damokradiyya ba wai don su sauya mulkin zaluncin sojoji zuwa ga mulkin mutum daya bane. A’a! Zabin damokradiyya ya kasance domin dawo da mulki ga mutane ne,” inji shi.

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, manufar ranar 12 ga watan Yuni ba wai kaddamar dashi a matsayin ranar Damokradiyya bane kawai. Yace akan na tattare da abunda yafi hakan.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa 12 ga watan Yuni yafi 29 ga watan Mayu muhimmanci - Babban jigon APC na kasa

Atiku ya caccaki gwamnatin Buhari, cewa a yanzu Najeriya ce hedkwatar tsantsar talauci a duniya. Yace ta yaya za a yi ace an kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu alhalin al’umman kasar na tunanin ta ina abincinsu na gaba zai fito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel