Okorocha ya yiwa INEC godiyar bashi takardar shaidar cin zabe

Okorocha ya yiwa INEC godiyar bashi takardar shaidar cin zabe

A ranar Talata, 11 ga watan Yunin 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta mallakawa tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha takadar shaidar cin zaben kujerar Sanata da aka gudanar a watan Fabrairu.

Hukumar INEC a baya ta hau kujerar naki ta mallakawa tsohon gwamnan Imo takardar shaidar cin zabe a sakamakon zargin sa da tursasa wa babban baturen zabe na jihar, Farfesa Innocent Ibeabuchi shelanta nasarar sa.

Babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja a ranar Juma'ar da ta gabata, ta umurci hukumar zabe ta kasa da ta gaggauta mallaka wa tsohon gwamna Okorocha takardar shaidar lashe zaben kujerar sanatan shiyyar Imo ta Yamma.

Cikin hukuncin da alkalin kotun, Justice Okon Abang ya zartar, ya ce hukumar INEC ba ta da dalilin hana tsohon gwamnan jihar Imo takardar sa ta shaidar cin zabe bayan da nasarar sa ta tabbata.

KARANTA KUMA: Tun daga kan shugaba ake fara yakar cin hanci da rashawa - Kagame

Yayin bayyana farin cikin sa, zababben Sanatan shiyyar Imo ta Yamma, ya mika godiya ta musamman ga babbar kotun tarayya da kuma hukumar INEC dangane da mallaka masa takardar shaidar cin zabe.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Okorocha ya mika godiyar sa cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Sam Onmuemedo, ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a birnin Owerri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel