Me ya faru: An nemi Obasanjo, Jonathan, Gowon, AbdusSalam an rasa a Eagle Square

Me ya faru: An nemi Obasanjo, Jonathan, Gowon, AbdusSalam an rasa a Eagle Square

Yayinda bikin ranar Demokradiyya ya kankama a farfajiyar Eagle square dake babbar birnin tarayya Abuja, an nemi dukkan tsafin shugabannnin kasar Najeriya an rasa a taron duk da an ajiye musu kujeru.

Wannan abu ya zo da mamaki kasancewar manyan al'umma kuma manyan abokan marigayi Cif MKO Abiola wanda saboda gwagwarmayarsa aka canza ranar demokradiya zuwa ranar 12 ga Yuni.

Tsaffin shugabannin kasan sune, Janar Yakubu Gowon, Janar Abdus salam Abubakar, Janar Ibrahim Babangida, Cif Olusegun Obasanjo, da Cif Ernest Shonekan.

KU KARANTA: KAI TSAYE: Yadda ranar demokradiyya ke gudana a farfajiyar Eagle Square

Alkaluma sun bayyana cewa Obasanjo ya ki halartan taron ne saboda kunya. Ya kasance wanda ya ci gajiyar marigayi Abiola amma har ya gama mulkinsa bai iya yin abinda shugaba Muhammadu Buhari yayi ba.

Shi kuma Cif Ernest Shonekan, an siffatashi matsayi daga daya cikin wadanda suka yaudari Abiola da yan Najeriya saboda son mulki.

Hakazalika Janar Ibrahim Babangida, ba zai iya halarta ba saboda shine ummul haba'isin soke zaben da Abiola ya samu nasara wanda hakan ya kai ga rasa rayuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel