Rashin imani: Shugaban makaranta ya yiwa dalibarsa ‘yar shekara 4 fyade

Rashin imani: Shugaban makaranta ya yiwa dalibarsa ‘yar shekara 4 fyade

Jami’an yan sanda sunacafke wani mutumi mai suna Abubakar Haruna, wanda ya kasance Shugaban makarantar Nursery and Baby Care and Primary School da ke anguwar Jaba karamar hukumar Sabon Gari, bisa zargin yiwa dalibarsa yar shekara hudu fyade.

An tattaro cewa mumunan al’amarin ya afku ne a harabar makarantar inda mahaifin yarinyar ya kai rahoton lamarin ga ofishin yan sanda da ke kasuwar mata na Sabon Gari a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni.

Mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim Salisu ya sanar da yan sandan cewa Haruna ya lalata masa yarsa don haka su kuma suka kama shi.

Bayan kamun Haruna da yan sanda suka yi, ya amsa laifinsa inda aka tura yarinyar zuwa asibiti domin samun sakamakon likita.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa 12 ga watan Yuni yafi 29 ga watan Mayu muhimmanci - Babban jigon APC na kasa

Bayan gwaje-gwajen da likitoci suka yi, sun bayyana cewa an auna arziki domin bai yi mata lahani ba sosai, inda suka bayar da ranar da za a dawo domin karban sakamakon gwajin da suka yi.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa a yanzu haka malamin na a hannun yan sanda inda suka tsare shi yayinda ake jiran sakamakon asibitin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel