Da duminsa: Yadda aka rabawa 'yan majalisu cin hancin daloli domin su zabi Gbajabiamila

Da duminsa: Yadda aka rabawa 'yan majalisu cin hancin daloli domin su zabi Gbajabiamila

- Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa an kama 'yan majalisu dumu-dumu suna raba dalolin da aka basu cin hanci don su zabi Femi Gbajabiamila

- Jaridar ta bayyana cewa bayan dalolin da aka basu an bai wa kowannen su kati na cire kudi, wanda aka sanya makudan kudade a ciki

An samu kwararan shaidu dake nuna yadda aka dinga rabawa tsofaffin 'yan majalisar dokoki da sababbi kudi domin su zabi Femi Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisar wakilai ta kasa.

Jaridar Sahara Reporters ta tabbatar da cewa an bai wa kowanne dan majalisa katin cire kudi, wanda aka sanya kudi masu tarin yawa a cikin kowanne, domin jawo hankalin su wurin zabar dan majalisar.

Duk da dai jaridar tace ba za ta iya saurin yanke hukunci akan ko nawa ne a cikin kowanne kati ba, amma tana da tabbacin cewa akwai makudan kudade a ciki.

Katin wanda aka sanya masa suna 'Member's Green Card' a turance sannan a kasa an sanya sunan Femi Gbajabiamila da Ahmed Wase, da kwanan wata.

KU KARANTA: Abin da mamaki: Wani mai kudi ya saci kaza don ya sayar ya sayi man da zai sanyawa motar da ya saya naira miliyan 140

An raba katin ga wadanda tun farko suka nuna goyon bayansu ga Gbajabiamila, sannan kuma suka nuna suna tare dashi a kowanne hali.

Kafin a fara gabatar da zaben Kakakin majalisar, an hango da yawa daga cikin 'yan majalisar a bangaren bandakin maza na majalisar suna raba daloli ga junansu.

Idan ba manta ba kimanin 'yan majalisar tarayya 66 ne suka zabi Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa, kuma anyi zargin cewa an bai wa kowannen su naira miliyan 25 domin su zabe shi.

Gbajabiamila ya lashe zaben Kakakin majalisar da kuri'u 281, yayin da abokin hamayyarsa Umar Bago ya samu kuri'u 78.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel