KAI TSAYE: Yadda ranar demokradiyya ke gudana a farfajiyar Eagle Square

KAI TSAYE: Yadda ranar demokradiyya ke gudana a farfajiyar Eagle Square

Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kasar Laberiya, George Weah, shugaban kasar Nijar, Mohammad Issoufou, shugaban kasar Ruwanda, Paul Kagame, sun isa farfajiyar Eagle Square.

A ranar 6 ga watan Yuni, 2018, shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da ranar ga Yuni matsayin sabon ranar murnan demokradiyya.

Shekara daya bayan wannan sanarwa, shugaba Buhari a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni ya rattaba hannu kan dokar mayar da ranar 12 ga Yuni ranar hutu.

A sabuwar dokar, game da cewar hadimin shugaba Buhari kan harkokin majalisar dokoki, Ita Enang, an soke ranar 29 ga Mayu matsayin ranar hutu da demokradiyya. Innama za'a mika mulki ne kawai ranar.

A ranar 12 ga watan Yuni, 2019, Moshood Kashimawo Abiola ya lashe zaben shugaban kasa inda mutan Najeriya daga kowani lungu da sako suka zabesa tare da mataimakinsa, Babagana Kingigbe.

Amma, zaben wacce ake siffatawa matsayin zabe mafi gaskiya a tarinin Najeriya, shugaban kasar mulkin soja a lokacin, Ibrahim Badamasi Babangida, ya soke zaben.

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel