Atiku yayi dai-dai da ya kalubalanci nasarar Buhari - Jonathan

Atiku yayi dai-dai da ya kalubalanci nasarar Buhari - Jonathan

-Jonathan ya goyi bayan Atiku dangane da karar da ya kai kotu na kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019

-Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da ya sanya ya yarda da kayin da Buhari yayi masa a zaben Shugaban kasa na 2015

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce Atiku Abubakar ya yi dai-dai da ya kalubalanci nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben da aka gudanar a cikin watan Fabrairu, inda yake cewa ba dai dai bane a kamanta yanayin zaben Atiku da yanayin zaben 2015, wanda ya sha kaye.

Jonathan ya ce dalilan da suka sanya ya zama shugaba na farko a Najeriya da ya sha kayi yana kan kujera a zaben 2015 ba daya bane da na zaben 2019.

Ya ce zaben 2019 cike yake da tashe tashen hankali da magudin zabe. “Ba dai dai bane a kamanta sakamakon zaben 2015 da matsayar Atiku kan zaben 2019 saboda akwai ban ban ci tsakaninsu." Jonathan ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da Premium Times don bugawa a wata mujalla ta bikin murnan cika shekara 20 a lardin Najeriya na hudu.

KARANTA WANNAN: Har yanzu ba a gano Magajin Garin Daura ba, kwana 43 da dauke shi

Jonathan ya ce aikinshi ne ya tabbatar da cewa anyi zabe ingantacce cikin lumana karkashin jagorancinshi, duk da cewa hukumar zabe zaman kanta take.

A shekarar 2015, nine shugaban kasa, duk da cewa hukumar zabe zaman kanta take, kowanne bangaren gwamnati a karkashin iko na yake

A lokacin nine shugaban kasa kuma INEC ta gudanar da zabe karkashin kulawa ta. Atiku ko bashi ne shugaban kasa ba, sabida haka idan shi ko jam’iyyarshi suka ga ba ayi dai dai ba, suna da ikon su kalubalanci zaben a kotu

Jonathan ya bayyana mulkinsa a matsayin na daban a tarihin Najeriya kuma ya yabi gwamnatinsa inda yake cewa ya tafiyar da tattalin arzikin kasa mai dunbin cigaba.

Najeria ce kasar da kasashen waje suka fi zuba hannun jari lokacin mulki na. An bayyana mu a mtsayin kasar da tafi ko wacce karfin tattalin arziki a Afirika, mun habbaka harkar noma kuma mun wadatar da kasar da abinci.”

Tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa cigaban da suka kawo a mulkinsa har yanzu ba a samu wani cigaba ba, ya kuma kara da cewa akwai canje canje da yawa da ake bukatar ayi.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwer :http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel