Dalilin da yasa 12 ga watan Yuni yafi 29 ga watan Mayu muhimmanci - Babban jigon APC na kasa

Dalilin da yasa 12 ga watan Yuni yafi 29 ga watan Mayu muhimmanci - Babban jigon APC na kasa

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya jinjina wa ci gaban da aka samu a damokradiyyar kasar, cewa muhimmancin da ke tattare da shi, hatta ranar 29 ga watan Mayu bai kai ranar 12 ga watan Yuni muhimmanci ba a tarihin damokradiyyar kasar.

Tiubu ya bayyana hakan a wani jawabi na musamman kan bikin ranar 12 ga watan Yuni mai taken: ‘June 12: The truth that sets democracy free in our land’.

A cewarsa, abunda kasar ke gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayun kowace shekara tun bayan samun damokradiyya a 1999 ya kasance ranar mika mulki ne kawai daga mulkin soja zuwa na zababben gwamnatin farar hula.

Jigon na APC yace raya ranar 29 ga wan Mayu a matsayin ranar Damokradiyya ya kaucema yanayin da damokradiyyar kasar ta tsinci kanta tun a shekarar 1999 daga gwagwarmaya mai daci kan mulkin soja daga ranar 12 ga watan Yuni, 1993, har bayan gushewar mulkin soja ta karfin tsiya a 1999.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye adon tafiya: Muhimman batutuwa 19 game da zaben ‘June 12 1993’

Ya bukaci yan Najeriya da kada su dauki lamarin damokradiyya da suke ciki a yanzu da wasa ko kuma yin wani ab da zai zama barazana ga kasancewarta, cewa ba cikin sauki da zaman lafiya aka same ta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel