Allah ya kiyaye gaba: An kone kasuwa yayin wani rikici da ya ritsa da Hausawa a jihar Osun

Allah ya kiyaye gaba: An kone kasuwa yayin wani rikici da ya ritsa da Hausawa a jihar Osun

- Wani rikici da ya barke a jihar Osun yayi sanadiyyar kone gidaje da shaguna

- Rikicin wanda ya samo asali tsakanin matasan Hausawa da Yarabawa

- Yanzu haka dai jami'an tsaro sun shiga tsakani komai ya dawo daidai a yankin

An kone kasuwar Sabo dake Ifewara, helkwatar karamar hukumar Atakumosa ta yamma, cikin jihar Osun, bayan wani mummunan rikici da ya barke tsakanin wasu matasan Hausa da Yarabawa.

Iferawa shine mahaifar Fasto Enoch Adeboye, babban Faston Cocin Redemeed Christian Church.

Duk da dai an dan samu sabani akan abinda ya kawo rikicin ranar Talatar nan da ta gabata, amma rahotanni sun bayyana cewa wasu matasan Hausa sun kaiwa wani mutumi mai suna Demola hari, a yankin Oke Oguro, wani kauye dake karkashin Iferawa, jaridar Punch ta sanar da haka.

KU KARANTA: Sani Haruna: Ban san yawan mutanen dana kashe ba a shekara daya

Wani shaida a garin yace wasu Hausawa masu aiki a gurin hakar ma'adanai dake yankin Oke Oguro, sun kai wa Demola hari sannan sun dauke masa wasu kudade daga wurin sa.

Rahotanni sun nuna cewa bayan Demola ya samu ya gudu daga wajen Hausawan, sai yaje ya tattaro 'yan uwansa, suka kaiwa unguwar da Hausawa suke yin sana'o'insu.

Wani mazaunin garin mai suna Gbeminiyi yace an kone wani gida a Sabo, amma saboda wutar ta kama da yawa yasa ta shafi wasu shaguna dake kusa da gidan.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, FOlasade Odoro, ya ce yanzu dai komai ya lafa a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel