Sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa sun kaiwa Buhari ziyarar ban godiya

Sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa sun kaiwa Buhari ziyarar ban godiya

- Sanata Ahmad Lawan ne sabon shugaban majalisar dokokin tarayya

- Wanda ake zargi da sace sandar majalisa ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa

Sabon zababben shugaban kasan majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, tare da sabon mataimakinsa, Ovie Omo Agege, sun kai ziyarar ban godiya ga shugaba Muhammadu Buhari kan rawar da ya taka wajen wannan nasara da suka samu.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncinsu ne da daren Talata, 11 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa dake Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa sun kaiwa Buhari ziyarar ban godiya

Sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa
Source: Facebook

Sanata Ahmad Lawan ya lashe zaben shugabancin majalisar da kuri'u 79 yayinda abokin hamayyarsa, Ali Ndume, ya samu kuri'u 28.

Hakazalika Sanata Ovie Omo Agege ya lashe zaben mataimakin shugaban majalisar ya lashe zaben da kuri'u 68 inda abokin hamayyarsa, Ike Ekweremadu, ya samu kuri'u 37.

Sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa sun kaiwa Buhari ziyarar ban godiya

sun kaiwa Buhari ziyarar ban godiya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel