Waiwaye adon tafiya: Muhimman batutuwa 19 game da zaben ‘June 12 1993’

Waiwaye adon tafiya: Muhimman batutuwa 19 game da zaben ‘June 12 1993’

Guda daga cikin zabukan da aka taba gudanarwa a Najeriya wanda duniya ta yi amanna cewa sahihin zabe ne da babu magudi a cikinsa shine zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 wanda ya gudana a zamin mulkin Janar Ibrahim Badamasa Babangida.

Tarihin Najeriya ba zai taba cika ba ba tare da ambaton wannan zabe ba, don haka Legit.ng ya binciko muku wasu muhimman bayanai guda 19 dangane da zaben ya zamto zakaran gwajin dafi a zabukan Najeriya, kamar haka;

KU KARANTA: Abubuwa 17 daya kamata ku sani game mutumin da Buhari ya karrama da ranar dimukradiyya

- Zaben 12 ga watan Yunin 1993 shine zabe na farko da aka yi a Najeriya tun bayan juyin mulkin 1983

- Shugaban hukumar zabe na wancan lokacin shine Farfesa Humphrey Nwosu

- A ranar 10 ga watan Yuni wata babbar kotun Abuja ta hana gudanar da zaben, amma hukumar zabe bata yi biyayya ga dokar ba

- Zaben ya gudana a ranar 12 ga watan Yuni tsakanin Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola daga jahar Ogun da Alhaji Bashir Tofa daga jahar Kano

- Abiola ya fito daga jam’iyyar SDP, yayin da Bashir Tofa ya fito daga jam’iyyar NRC

- Abiola ya samu nasara akan Atiku Abubakar da Babagana Kingigbe a zaben fidda gwanin SDP

- Bashir Tofa ya samu nasara akan Pere Ajunwa, Joe Nwodo da Dalhatu Tafida a zaben fidda gwani na NRC

- Shugaban yakin neman zaben Abiola shine Jonathan Zwingina

- Abiola ya zabi Babagana Kingigbe a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa

- Bashir Tofa ya zabi Sylvester Ugoh a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa

- Jami’in hukumar zabe mai sanar da sakamakon zabe shine Farfesa Felix Iredia

- A ranar 13 ga watan Yuni Felix Iredia ya dakatar da sanar da sakamakon zaben

- A ranar 16 ga watan Yuni hukumar zabe ta bayyana cewa ba zata sanar da sakamakon zaben ba

- Sakamakon da wata kungiya ta saki ya nuna Abiola ya samu kuri’u 8,341,309, Bashir Tofa ya samu 5,952,087

- A ranar 23 ga watan Yuni gwamnatin IBB ta soke sakamakon zaben bayan hukuncin kotu

- Rikicin siyasa ya kaure a Najeriya wanda yayi sanadiyyar murabus da IBB yayi a watan Agusta 1993, Abacha yah au mulki

- 1994 Abiola ya sanar da kansa a matsayin shugaban kasar Najeriya a Legas

- Abacha kamashi ya daureshi tsawon shekaru 4 a gidan kurkuku

- A ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1998 ya rasu a kurkuku yana dan shekara 60

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel