Har yanzu ba a gano Magajin Garin Daura ba, kwana 43 da dauke shi

Har yanzu ba a gano Magajin Garin Daura ba, kwana 43 da dauke shi

Hukumar yan sanda a jihar Katsina ta ce tayi kamen wasu mutane a binciken da takeyi na sace Magajin Garin Daura, Alhaji Umar Uba.

Kawo yanzu, kwana 43 kenan da sace Magajin garin wanda yan bindiga suka dauke a gaban gidanshi dake Daurama road da marecen rananr Laraba 1 Mayu, 2019.

Mai magana da yawun hukumar SP Gambo Isa ne ya bayyana kamen da a kayi amma bai zayyana suwa aka kama ba ko kuma abinda aka kwato a dalilin kada a bata binciken da su ke yi.

A cewarshi ”bamu so mu bata binciken da mukeyi” ya kara da cewa “muna jajantawa iyalansa, yanuwansa da abokan arziki bisa afkuwar lamarin, ba zamuyi kasa a gwuiwa ba har sai mun tabbata mun maidoshi ga iyalansa inshaAllah”

An shiga rudani sosai akan afkuwar lamarin, a inda wasu yan uwan Magajin garin ke cewa lamarin ya sha banban da sauran sace sacen da akeyi, kasancewar har yanzu yan bindigar basu tuntubi danginshi ba.

KARANTA : Yadda Yansanda suka yi caraf da wani dalibin jami’a dauke da makamai da kayan Sojoji

A lokacin da aka tunttubi Dan Lawan Daura, Umar Umar Ata, wanda kane ne ga wanda aka sace, ya ce har yanzu basu ji komi game dashi ba.

Mun mika lamarin ga ubangiji muna kuma rokon Allah ya maidoshi gida lafiya.”

Wani na kusa da iyalan wanda aka sace ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa iyalan na cikin wani hali.

“ Suna cikin tashin hankali har aka gama azumin Ramalana akayi karamar sakka kasancewar babu wani sanannen lamari game dashi”

A sabida hakanan ne ma ba ayi wasu shagulgulan sallah ba duk da cewa iyalan sun dabbaka al’adar magajin garin na taimakawa talakawa a lokutan azumi da sallah, sun rarraba kayan abinci kamar yadda aka saba kuma an tsawaita addu’ar Allah ya maidoshi lafiya

Magajin Gari kane ne ga sarkin Daura Alhaji faruk Umar faruk. Tshon jami’in kwastam ne kuma miji ne ga Hajiya Bilki, diya ga yar uwar Shugaba Muhammadu Buhari. Shine kuma mahaifin Fatima matar dogarin shugaban kasa Buhari, Col. Muhammad Abubakar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe: http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel