Abubuwa 17 daya kamata ku sani game mutumin da Buhari ya karrama da ranar dimukradiyya

Abubuwa 17 daya kamata ku sani game mutumin da Buhari ya karrama da ranar dimukradiyya

Yau Laraba, 12 ga watan Yuni itace karo na farko da za’a fara bikin ranar Dimukradiyya a wannan rana kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bayan ya rattafa hannu akan dokar data tabbatar da haka don karrama marigayi Cif MKO Abiola.

Da wannan ne Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman bayanai game da Abiola don fahimtar muhimmancinsa da matsayinsa a Najeriya da har gwamnatin Najeriya ta yi masa wannan karramawa data sauya ranar dimukradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga Yuni.

KU KARANTA: Wasu muhimman bayanai guda 7 game da Abiola, mutumin Buhari ya karrama

- A ranar 24 ga watan Agustan 1937 aka haifi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola.

- Iyayensa sune Alhaji Salawu Abiola da Alhaja Zuliat Wuraola, kuma shine yaro na 23 a gidan.

- Yana dan shekara 9 ya fara fafutukar neman kudi ta sana’ar sayar da itace.

- Ya yi karatun Firamari a African Central School, Abeokuta, Sakandari a Baptist Boys High School Abeokuta, sai jami’ar Glasgow inda ya karanci kididdiga.

- Fitaccen attajiri ne, kuma hamshakin dan kasuwa ne, kuma mai taimakon jama’a

- Shine Aare Ona Kankafo, watau Sarkin yakin kasar Yarbawa

- Ya auri mata da dama a rayuwarsa, fitattu daga ciki sune Simbiat Atinuke Shoaga,

Kudirat Olayinka Adeyemi, Adebisi Olawunmi Oshin, Doyinsola Abiola Aboaba, Modupe Onitiri-Abiola, Remi Abiola.

- Ya haifi yaya da dama, daga cikinsu akwai Abdulateef Kola Abiola, Dupsy Abiola, Hafsat Abiola, Rinsola Abiola, Khafila Abiola.

- Ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 1993 a jam’iyyar SDP, zamanin mulkin janar Babangida

- IBB ya soke sakamakon zaben a ranar 12 ga watan Yuni 1993 yayin da Abiola yake kan gaba, ya sha gaban abokin karawarsa Bashir Tofa na jam’iyyar NRC

- Abiola ya samu kuri’u 8,341,309, Bashir Tofa ya samu 5,952,087 kafin dakatar da sanar da sakamakon zaben

- A 1994 ya sanar da kansa a matsayin shugaban kasa a unguwar Epetedo dake tsibirin jahar Legas

- Abacha ya aika da motocin Yansanda 200 domin su kamoshi

- An kashe matarsa Kudirat a shekarar 1996 yayin da take zanga zangar goyon bayansa

- Gwamnatin Abacha ta daureshi tsawon shekaru 4 a gidan kurkuku

- A ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1998 ya rasu a kurkuku yana dan shekara 60

- Buhari ya karramashi da lambar yabo mafi girma na GCFR a ranar 5 ga watan Yunin 2018

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel