EFCC: An canza Alkalin da ke binciken Ayo Fayose a Kotu

EFCC: An canza Alkalin da ke binciken Ayo Fayose a Kotu

Wani babban kotun tarayya da ke Legas ya sa ranar da za a cigaba da shari’a tsakanin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa da kuma tsohon gwamna Ayodele Fayose.

Wannan labari ya zo mana ne daga jaridar Daily Nigerian a Ranar Talata 11 ga Watan Yunin 2019. Babban kotun zai cigaba da zama ne a Ranar Juma'a 28 ga Watan Yuni, 2019, kamar yadda Alkali ya fada.

Alkali mai shari’a Mojisola Olatotegun ce ta fara binciken karar da EFCC ta kawo na Ayo Fayose da wani kamfani mai suna Spotless Investment Ltd. An shigar da wannan kara ne tun a watan Oktoban 2018.

Daga baya an dauke shari’ar daga hannun mai shari’a Olatoregun zuwa ga wani Alkali dabam, Chukwujekwu Aneke, bayan kukan da EFCC ta kai gaban babban Alkalin kotun watau A. Abdu-Kafarati.

KU KARANTA: INEC ta bi umarnin kotu, ta ba Okorocha satifiket

EFCC ta na zargin Ayo Fayose da wasu laifuffuka 11, daga ciki akwai zargin karbar makudan kudi da su ka kai har Dala miliyan 5 daga hannun tsohon Minista Musiliu Obanikoro, ba tare da bin ka’ida ba.

Kwanaki an samu matsala tsakanin Lauyoyin EFCC masu kara da kuma Alkali. Wannan ya sa su ka nemi a sake Alkali bayan sun ga alamun cewa wanda ke kula da shari’ar ba za ta yi abin da ya dace ba.

Sabon Alkali mai shari’a ya bada kwanaki 16 ne domin a zauna da Ayo Fayose, wanda ake zargi. Za a sake gurfanar da wanda ake tuhuma, tsohon gwamnan Ekiti ne a karshen wannan watan mai-ci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel