KEDCO ta kaddamar da tiranfomomi 170 da motocin aiki 60

KEDCO ta kaddamar da tiranfomomi 170 da motocin aiki 60

Kamfanin dillancin wutar lantarki na Kano (KEDCO) a ranar Talata 11, Yuni 2019 ya kaddamar da tiransfomomi 170 da motocin aiki 60 da wasu kayan aikin a kokarin sa na habbaka samuwar wutar lantarki a wuraren da kamfanin ke samarwa da wutar lantarki.

Babban daraktan kamfanin, Dr. Jamilu Gwamna ya bayyana hakan a lokacin da ake kaddamar da kayayyakin aikin a ofishin kamfanin dake kusa da gadar Ado Bayero a cikin garin Kano.

Yace samar da kayayyakin aikin na daga cikin kokarin da kamfanin keyi don inganta ayyukansa ga abokan huldarsa a garuruwa uku da yake aiki.

“ Baza mu iya cimma kudirorin mu ba har sai mun samu isassun kayan aikin da zamu gudanar da aiki ba tare da matsala ba.

Muna fata abokan huldarmu zasu saka mana da alkairi wajen biyan kudin wutar lantarki cikin lokaci” inji Gwamna.

Karanta wanna: Sojoji sun tseratar da mata da kananan yara yayin da suka yi kicibus da Boko Haram

Ya bayyana yakininshi na cewa kamfanin nasu na daya daga cikin kamfanoni masu kyau cikin kamfanonin dillacin wutar lantarki (DISCOS) a Najeriya.

Ya bukaci ma’aikatansu da su kara jajircewa akan ayyukansu da kuma magance matsalolin abokan huldarsu cikin llokaci.

Akan masu korafi cewa kudin lantarkin ya yi yawa, babban daraktan yayi kira ga masu wannan koken dasu je ofishin KEDCO mafi kusa dasu, su bayar da sunayensu don su samu mita mai amfani da kati

Ya ce kwanannan hukumar lura da wutar lantarki ta najeriya (NERC) zata kaddamar da rabon mita mai amfani da kati a jihohin Kano, katsina da Jigawa.

Ya bayyana cewa Gidauniyar Shell da kamfanin zasu zuba kudi Dalal Amurka biliya biyu a kamfanin don ganin an ingata samun wutar lantarki.(NAN)

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe: http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel