Sojoji sun tseratar da mata da kananan yara yayin da suka yi kicibus da Boko Haram

Sojoji sun tseratar da mata da kananan yara yayin da suka yi kicibus da Boko Haram

Dakarun rundunar Sojan Najeriya sun kaddamar da wani harin kwantan bauna akan wasu ayarin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram yayin da suke kokarin tserewa daga Sojojin, inda suke bude musu wuta tare da ceto mutane takwas da suke rike dasu.

Legit.ng ta ruwaito dakarun bataliya ta 121 tare da hadin gwiwar mafarauta ne suka samu wannan nasara a kauyen Gwadala, inda suka katse ma mayakan Boko Haram din hanzari ta hanyar yi musu luguden wuta har suka kashe daya daga cikinsu, yayin da jikkata sauran.

KU KARANTA: Saurayin daya rataye budurwarsa ya fuskanci matsanancin hukuncin kisa daga Kotu

Sojoji sun tseratar da mata da kananan yara yayin da suka yi kicibus da Boko Haram

Mata 2 da kananan yara 6
Source: Facebook

A yayin wannan hari, Sojoji sun ceto wasu mutane Takwas da yayan kungiyar ta’addancin suke rike dasu, daga cikinsu akwai mata guda biyu da kananan yara guda shida, bugu da kari Sojojin sun kwato kayayyaki daga wajen yan ta’addan kamar haka:

- Bindigar AK 47

- Bindigar toka

- Alburusai da dama

Sabon salon yakin da rundunar Soja ta kirkiro na kakkabe ragowa yan ta’adda a duk inda suke yana samar da sakamako mai kyau musamman tun bayan kaddamar da aikin ‘Operation Halaka dodo’, kamar yadda kwamandan yaki, Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu ya bayyana.

Sojoji sun tseratar da mata da kananan yara yayin da suka yi kicibus da Boko Haram

Makamai
Source: Facebook

Birgediyan ya jinjina ma dakarun Sojin dake gudanar da aikin kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, inda ya bayyana musu cewa babban hafsan sojan kasa, Tukur Buratai ma na jinjina musu.

Daga karshe rundunar ta yi kira ga jama’an dake zaune a yankin dasu taimaka ma hukumomin tsaro da muhimman bayanai da zasu taimaka musu wajen gudanar da aikin kawar da yan ta’adda, tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da kuma dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel