Yadda Yansanda suka yi caraf da wani dalibin jami’a dauke da makamai da kayan Sojoji

Yadda Yansanda suka yi caraf da wani dalibin jami’a dauke da makamai da kayan Sojoji

Masu iya magana kan ce kwana dubu na barawo, kwana daya rak na mai kaya, rundunar Yansandan jahar Cross River ta yi nasarar cafke wani dalibin jami’a dsake karatun likitanci a jami’ar Calabar da laifin mallakan muggan makamai.

Rahoton kamfanin dillancin labaru ta bayyana cewa baya ga tuhumar mallakar makamai, rundunar tana tuhumar dalibin da laifin kasancewa dan kungiyar matsafa, wanda shi kansa wannan laifi ne mai zaman kansa.

KU KARANTA: Saurayin daya rataye budurwarsa ya fuskanci matsanancin hukuncin kisa daga Kotu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan, DSP Irene Ugbo ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa data fitar a ranar Talata, 11 ga watan Yuni a babban ofishin Yansandan jahar dake garin Calabar.

Irene tace dalibin da ba’a bayyana sunansa bay a fada hannun runduna ta musamman dake yaki da miyagun ayyukan garkuwa da mutane da shiga kungiyoyin asiri ne a yayin da suke gudanar da sintiri.

Daga cikin abubuwan da rundunar ta kwato daga wajen dalibin akwai karamar bindiga guda daya, alburusai, tabar wiwi guda bakwai, kayan kungiyar matsafa ta Aiye, da kuma kayan Sojoji guda biyu.

Daga karshe kaakakin tace dalibin ya amsa laifinsa, kuma tuni suka kaddamar da bincike akansa, tare da shirin gurfanar dashi gaban kotu da zarar binciken ya kammala.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne aka samu wani direban bankaura ya tattake wani dalibin jami’ar Calabar da mota yayin da yake zaman zamansa a cikin jami’ar inda ya kasheshi har lahira.

Kaakakin Yansandan jahar ta bayyana cewa bincike ya nuna direban sai da yayi tatil da barasa, sa’annan yayi mankas kafin ya hau motar yana marisa yana layi, hakan ne yayi sanadiyyar kwacewar motar daga hannunsa har ta afka ma dalibin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel