Jawabin da Jam'iyyar PDP ta yi bayan nada sababbin shugabannin Majalisa

Jawabin da Jam'iyyar PDP ta yi bayan nada sababbin shugabannin Majalisa

Mun samu labari cewa jam’iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ta fito ta yi jawabi bayan Sanata Ahmad Lawan da Honarabul Femi Gbajabiamilla sun yi nasara zaben Majalisar tarayya da aka yi a makon nan.

A jiya Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019, aka rantsar da Ahmad Lawan da kuma Femi Gbajabiamilla a matsayin shugabannin majalisar dattawan Najeriya da kuma na wakilan tarayyar kasar nan.

Babbar jam’iyyar adawa ta kasar watau PDP, ta taya sababbin shugabannin kasar murnar lashe zabe da kuma darewa kan kujera. PDP tayi wannan jawabi ne ta bakin jami’in ta Kola Ologbondiyan.

Ologbondiyan, wanda shi ne sakataren yada labarai na PDP na kasa, ya taya sabon shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, da kuma kakakin majalisar wakilan kasar da mataimakinsa murna.

Kola Ologbondiyan ya ce:

KU KARANTA: ‘Yan PDP sun tuburewa Jam’iyya sun goyi bayan ‘Yan takaran APC

“PDP ta na jinjinawa wadanda su ka yi ruwa da tsaki wajen ganin damukaradiyya ya kai inda ya kai a yanzu.”

“Jam’iyyar PDP za ta cigaba da tsayawa kan gaskiya tare da kuma ganin daraja da kimar majalisar tarayya a Najeriya…”

Kakakin jam’iyyar adawar ya cigaba da cewa:

“Mu na kira ga wadanda aka zaba da su sa kishin kasa a gaban su, da kuma harkar walwalar al’ummar Najeriya a gaba da duk wani ra’ayinsu.”

"…su tabbata wajen ganin majalisa ta samu cin gashin kan-ta, wanda shi ne kashin-bayan tsarin damukaradiyya da kuma tsarin mulkin Najeriya.”

PDP ta ke cewa:

“Dole wannan majalisa ta tara ta yi kokari wajen ceto kasar nan daga halin ha’ula’in da gwamnatin shugaba Buhari ta jefa kasar, ta hanyar tabbatar da nagartaccen mulki da kawo tsantseni a gwamnati, game da maganin satar dukiyar al’umma da kuma hana wuce gona da iri."

A na ta bangaren ,jam’iyyar PDP ta ce ta na nan a kan wadannan akidu na kare damukaradiyya, sannan ta ce ta na sa ran Atiku zai karbe nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben bana ta hanyar kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel