An gano yadda aka bawa 'yan majalisa toshiyar baki don zaben Gbajabiamila

An gano yadda aka bawa 'yan majalisa toshiyar baki don zaben Gbajabiamila

Ana ta kara samun bayannai kan yadda aka bawa zababun 'yan majalisar wakilai na tarayya katin sayaya domin su zabi Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar.

Sahara Reporters ta ruwaito cewar ta samu tabbas na cewa an raba wa dukkan 'yan majalisar kati mai dauke da kudade (Dallar Amurka) a matsayin toshiyar baki saboda a saya kuri'arsu.

Sai dai kawo yanzu ba a tabbatar da adadin kudaden da kowanne katin ke dauke da shi ba.

Katin da aka yi rubutu na musamman a jikinsa da 'Members Green Card' yana dauke da taken kamfen din Femi Gbajabiamila, wato 'Nation Building A Joint Task'.

DUBA WANNAN: Abubawa 5 da ya kamata ku sani kan sabon kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila

Kazalika, an rubuta 'Femi Gbajabiamila/Ahmed Wase' a jikin katin mai dauke da lamba ta musamman da kwanan wata. An yi rabon katin ne ga wadanda suka yi alkawarin zaben Gbajabiamila da Wase ne kafin rantsarwa a ranar Talata.

Kafin fara kada kuri'a a zaben kakakin majalisar an hangi wasu 'yan majalisar suna cika aljihunansu da daloli cikin takarda mai ruwan kasa.

Wannan toshiyar bakin da aka bawa 'yan majalisar ya saka su nuna takardan kada kuri'arsu domin bayyana wanda suka zaba domin gamsar da wadanda suka basu toshiyar bakin.

Idan ba a manta ba anyi ikirarin cewa an bawa 'yan majalisa 66 da suka goyi bayan takarar Sanata Ahmed Lawan Naira Miliyan 25 kowanensu a matsayin toshiyar baki.

Gbajabiamila ya yi nasarar zama kakakin majalisa da kuri'u 281 inda ya doke abokin hammayar sa Umar Bago da ya samu kuri'u 78.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel