INEC ta sha alwashin kallubalantar bawa Okorocha shaidar lashe zabe

INEC ta sha alwashin kallubalantar bawa Okorocha shaidar lashe zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta bayar na tilasta mata bawa tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha takardan shaidan cin zabe.

Okorocha ya karbi takardan shaidan lashe zabe a mastsayin wanda ya yi nasara a zaben sanata mai wakiltan yankin Imo ta Yamma a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

INEC ta bayyana hakan ne cikin jawabin da Kwamishinan kuma Ciyaman na Sadarwa na Wayar da kan Masu Zabe na hukumar, Mr Festus Okoye ya yi a ranar Talata a Abuja.

DUBA WANNAN: Sojoji sun gano shirin kungiyar ISWAP na daukan sabbin mayaka

Ya ce hukumar ta bawa Okorocha takardan shaidan cin zabe ne don yin biyaya ga umurnin Babban Kotun da ke Abuja da ya bukaci tayi hakan.

Okoye ya ci bawa Okorocha shaidan cin zabe ya nuna biyaya ga umurnin kotu da hukumar ke yi ko a lokutan da ba ta gamsu da wasu abubuwa ba.

Ya ce hukumar ta cimma matsayar bawa Okorocha shaidan lashe zaben ne a ranar Talata bayan sunyi taro sun tattauna kan wasu dalilai 14 da suka shafi batutuwan zaben.

Ya ce hukumar ta cimma matsayar bawa Okorocha shaidan lashe zaben ne a ranar Talata bayan sunyi taro sun tattauna kan wasu dalilai 14 da suka shafi batutuwan zaben.

"Mun duba hukunce-hukuncen da kotu suka yanke kan batun musamman wanda Babban Kotun Tarayya na Abuja ta yanke kan zaben mazabar Imo ta Yamma.

"Hukumar ta cimma matsayin bawa wanda ya shigar da karar, Rochas Okorocha takardan shaidan cin zabe domin biyaya ga hukuncin Mai Shari'a Okon Abang.

"Sai dai hukumar za ta daukaka kara a kan hukunciun."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel