Majalisa ta tara: Abinda nasarar Lawan da Gbajabiamila ke nuni - Dogara

Majalisa ta tara: Abinda nasarar Lawan da Gbajabiamila ke nuni - Dogara

Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar tarayya, ya taya sanata Ahmad Lawan da dan majalisa Femi Gbajabiamila murnar nasarar da suka samu na darewa kujerar shugabancin majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.

Dogara ya kuma taya sanata Ovie Omo-Agege da dan majalisa Ahmed Idris Wase murnar samun nasarar darewa kujerun mataimakin shugaban majalisar dattawa da mataimakin kakakin majalisar tarayya

A jawabin da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Turaki Hassan, a ranar talata, Dogara ya bayyana nasarar sababbin shuwagabannin majalisar a matsayin abinda mafi rinjayen sanatoci da yan majalisu ke so.

Karanta wannan: Majalisa: Bukola Saraki ya yi wa Lawan da Gbajabiamila nasiha

Dogara wanda ya kayar da Gbajabiamila a zaben kakakin majalisar wakilai a 2015, ya roki Allah ya taya sababbin shuwagabannin riko.

Tsohon kakakin majalisar, ya kara tabbatar da kudirinsa na taimakawa majalisar ta tara wajen ganin an tabbatar da akidu na dimukaradiyya don kawo cigaba a Najeriya.

Bayanin na cewa “Ina fatan majalisar ta tara, karkashin shuwagabanninta zasu karfafa cigaban da majalisa ta takwas ta samar har ma su dara ta.”

Yakubu Dogara ya kara da cewa “Muna rokon Allah ya basu iko da karfin gudanar da sha'anin majalisun guda biyu su kuma bada gudunmuwarsu wajen cigaban kasar nan, kuma a shirye nike da in basu gudunmuwa a koda yaushe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel