Obasanjo ya fadi wurin da gwamnatin Buhari zata kai Najeriya

Obasanjo ya fadi wurin da gwamnatin Buhari zata kai Najeriya

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce babu inda gwamnatin shugaba Buhari zata kai Najeriya sai cikin halin rashin tabbas da annoba.

Obasanjo ya fadi hakan ne a wata hira mai tsawo da jaridar Premium Times ta yi da shi a gidansu na gado dake karamar hukumar Ifo a jihar Ogun, a watan Mayu.

Jaridar ta gana da Obasanjo ne a shirinta na musamman domin taya Najeriya murnar cika shekaru 20 a mulkin dimokradiyya.

Sabani ya shiga tsakanin Obasanjo da Buhari gabanin zaben sheakarar 2019, lamarin da ya saka shi mara wa Atiku Abubakar, tsohon mataimakinsa da ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyya PDP, baya a zaben 2019.

DUBA WANNAN: Gbajabiamila ya bawa dan arewa babban mukami jim kadan bayan ya zama shugaban majalisar wakilai

Da yake magana yayin ganawar, Obasanjo ya bayyana cewar duk da an samu cigaba a Najeriya tun bayan dawowa mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, salon da gwamnatin Buhari ta dauka zai jefa kasa cikin annoba da rashin tabbas.

"Maslaha daya ce, dora Najeriya a turbar cigaba mai dorewa amma a halin da gwamnati mai ci ke tafiyar al'amuran kasa, ba mu san ida aka nufa ba.

"Ba mu da wani zabi da ya wuce mu dora Najeriya a kan turbar cigaba mai dore wa. Mun fara hakan tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999. Amma yanzu salon mulkin wannan gwamnatin na mayar da al'amura baya. A takaice, salon tafiyar gwamnatin babu inda zai kai kasa sai cikin halin 'ni 'ya su', annoba da rashin tabbas," a cewar Obasanjo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel