Wata kotu ta umarci INEC kar ta baiwa Okorocha takardar shedar zabe

Wata kotu ta umarci INEC kar ta baiwa Okorocha takardar shedar zabe

- An samu tanakudi tsakanin kotunan Najeriya biyu

- Bayan hanashi kada kuri'arsa a majalisa yau, wata kotu ta amsa bukatar abokin hamayyar Okorocha

Babbar kotun Imo ta umurci INEC kar ta baiwa Rochas Okorocha takardar shedar zabe a matsayin sanata mai wakiltar Imo ta yamma.

Mai shari’a Ngozi Ukoha ta dakatar da INEC daga shirinta na bayar da takardar zaben sanatan Imo ta yamma.

Kotun ta bayarda umurnin ne bayan da aka saurari kudirin da Osita Izunaso na jam’iyyar APGA ya shigar kafin sauraren cikakkiyar shari’ar wacce ke kalubalantar nasarar Okorocha na jam’iyyar APC.

Hukumar zaben ta ki bawa Rochas Okorocha shedar nasararsa bayan da jam’in hukumar ya kai rahoto kan cewa ya sanarda da sakamakon zaben cikin matsi daga Rochas Okorocha.

Karanta wannan: APC tayi murna kan nasarar da Lawan da Gbajabiamila suka samu

INEC, tace zata zauna don duba umarnin da wata babbar kotun tarayya ta Abuja ta bayar kan cewa a baiwa Rochas Okorocha shedar nasararsa.

Wannan sabon umarnin dake zuwa daga kotun shine na uku kan batun, bayan da wata babbar kotun tarayya a 23, Mayu ta umarci INEC kada ta bayar da shaidar zaben ga kowanne dan takarkarun.

Ana tsammanin INEC ta sanar da matsayarta game da batun a yau Talata 11, yuni 2019.

A yau da safe ne aka ki tantance Rochas Okorocha bayan ya isa majalisra don a kaddamar dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel