Shugaba Buhari ya taya sabbin shugabannin majalisa murna, ya sake caccakan Saraki da Dogara

Shugaba Buhari ya taya sabbin shugabannin majalisa murna, ya sake caccakan Saraki da Dogara

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya sabbin zababbabun shugabannin majalisar dokokin tarayya ta tara murnar nasarar zaben da ya gudana a yau Talata, 11 ga watan Yuni, 2019.

Buhari ya siffata nasararsu matsayin sabuwar alfijir, sabanin munafurci da barandancin wadanda suka shude.

Shugaban kasa ya yabawa dukkan yan majalisan da jam'iyyunsu kan nuna soyayyar su ga kasa kafin zabe da bayan zabe.

Ya yabi irin salon da akayi amfani da shi wajen gudanar da zaben, inda yace wannan babban nasarace ga demokradiyyar Najeriya.

Ya yi kira da zakarun zaben suyi amfani kujerarsu wajen fifita manufar kasa da jama'arta da kuma cigaban demokradiyya.

KU KARANTA: Da duminsa: Bayan tsawon lokacin tana jinya, an sallami Mama Taraba daga asibiti

A cewarsa: "Fadar shugaban kasa ba ta bukatar majalisar da zata rika juyawa. Duk da cewa ana son kowace bangare ta kasance da yancin kansa, akwai bukatar hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati."

Ya yi kira ga wadanda suka fadi zabe da su hada karfi da shugabanninsu wajen kawo cigaban kasa kuma ya bukaci zakarun su nuna girma.

Sabanin shekarar 2015, wannan karon shugaba Muhammadu ya saka hannu da baki tsundum cikin harkokin zaben shugabancin majalisar dokokin tarayya.

Ya yi kokarin hada kan dukkan mambobin APC dake majalisar har jajibirin zaben inda ya gana da dukkaninsu kan yadda abubuwa za su gudana. Ya la'anci shugabannin majalisar da ta shude bisa ga yadda suka mayar mas ada hannun agogo baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel