Da duminsa: Bayan tsawon lokaci tana jinya, an sallami Mama Taraba daga asibiti

Da duminsa: Bayan tsawon lokaci tana jinya, an sallami Mama Taraba daga asibiti

Bayan tsawon lokaci tana jinya a asibiti a kasar waje, tsohuwar ministar harkokin mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan, wacce akafi sani da Mama Taraba za ta dawo gida.

Mama Taraba ta bayyana hakan ne a ranar Talata, 11 ga wtaan Yuni, 2019 inda take mika godiya ga Allah madaukakin sarki kan lafiya da ta samu.

Tace: "Ga ni nan tare da likita na, Dakta Samir Tarabichi bayan an sallameni a yau, Alhamdu Lillah, abu ya yi kyau, Alhamdulillah."

Da duminsa: Bayan tsawon lokacin tana jinya, an sallami Mama Taraba daga asibiti

Da duminsa: Bayan tsawon lokacin tana jinya, an sallami Mama Taraba daga asibiti
Source: Facebook

KU KARANTA: Shikenan: Bayan shekaru 6, Kotu ta wanke Amina Dauda daga zargin kisan maigidanta

A kwanaki 29 da suka gabata, Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta nuna farin ciki da godiya ga dukkanin yan Najeriya da suka nuna kulawarsu da addu’o’i a gareta a lokacin da take fama da rashin lafiya.

Aisha ta bayyana a shafinta na Facebook cewa anyi mata aiki cikin nasara, kuma sannan ta ci gaba da samun sauki a kullun.

“Anyi mun aiki cikin nasara kuma ina samun sauki a kullun. Nagode gare ku kan addu’o’inku, yan uwa , abokan arzki da dukkanin yan Najeriya da suka nuna kulawa. Nagode sosai sosai. Miyetti.Jazakallah Khairan.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel