APC tayi murna kan nasarar da Lawan da Gbajabiamila suka samu

APC tayi murna kan nasarar da Lawan da Gbajabiamila suka samu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ondo ta bayyana nasarar Ahmed Lawan da Mista Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai kasa na tara a matsayin ni’ima a sabuwar sashin damukardiyya da cigaban Najeriya.

Mista Alex Kalejaiye, Sakataren sadarwa na jam’iyyar a jihar ne ya fadi haka a wani jawabin da ya gabatar ga manema labarai a ranar Talata, 11 ga watan Yuni a Akure.

Lawan ya samu kuri’u 79 inda ya doke Sanata Ali Ndume.

Ya bukaci yan Najeriya da su kyautata zatton samun wakilci nagari a majalisan dokokin kasar, ba tare da hana al’amuran da zasu kawo cigaba ba a kasar.

A cewarshi, Lawan ya sha daukar alkawarin jagorantar majalisar dattawa wacce za ta jajirce wajen aiki cikin aminci tare da sauran bangarori na gwamnati, ba tare da ya tauye hakkin bangaren dokoki ba.

Ya yabi kokarin dukkanin shugabanin jam’iyyar APC, musamman Kwamrad Adams Oshiomhole, da shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi bisa kokarinsu wanda ya cancanci yabo.

KU KARANTA KUMA: An kaddamar da Ahmed Wase a matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Ike Ekweremadu yace ya yanke shawarar takara ne domin yin zanga-zaga akan tsayar da Omo-Agege a matsayin wanda ake son ya dare kujerar mutum na biyu a majalisar dokokin tarayya na tara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel