Majalisa: Bukola Saraki ya yi wa Lawan da Gbajabiamila nasiha

Majalisa: Bukola Saraki ya yi wa Lawan da Gbajabiamila nasiha

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya taya sabon zababben shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, da mataimakainsa, Sanata Ovie Omo-Agege, da kuma sabon zababben shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da mataimakinsa, Idris Wase, murnar lashe zabe.

A sakon da ya fitar a shafinsa da Tuwita, Saraki, ya shaidawa sabbin shugabannin cewar sune zasu jagoranci majalisa karo na 9 na tsawon zango guda (shekara hudu).

"A yayinda zaku fara wannan muhimmiyar tafiya mai tsawon shekara hudu, ina mai kira a gare ku da ku saka Najeriya a ran ku da kuma kare kima da martabar majalisa a dukkan aiyukan ku.

"Ina mai fatan alheri a gare ku da dukkan ragowar Sanatoci da mambobin majalisar wakilai, ina yi muku fatan samun nasara a aiyukan da za ku yi na hidimtawa kasa," a cewar Saraki.

A gana wa ta karshe tsakanin bangaren zartar wa da shugabancin majalisa da aka yi cikin azumi a fadar shugaban kasa, shugaba Buhari ya ce bai ji dadin mulki da majalisar da Saraki da Dogara suka jagoranta ba.

A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan Talabijin na kasa (NTA), wacce sauran kafafen yada labarai suka watsa, Buhari ya ce ba zai saka Saraki da Dogara da majlisar tarayya karo na 8 a cikin 'yan kishin kasa ba.

DUBA WANNAN: Gbajabiamila ya bawa dan arewa babban mukami jim kadan bayan ya lashe zaben shugaban majalisar wakilai

Sanata Ahmed Lawan, danlelen shugaban kasa da jam'iyyar APC a zaben shugaban majalisar dattijai, ya samu nasarar buga abokin hamayyarsa da jam'iyyar PDP ke mara wa baya, sanata Ali Ndume, da kasa a zaben da aka yi yau, Talata.

Lawan ya zama sabon shugaban majalisar dattijai bayan ya samu adadin kuri'u 79, yayin da abokin takararsa kuma shalelen jam'iyyar PDP, Sanata Ndume, ya samu kuri'u 28 kacal.

Gbajabiamila, zabin jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa, ya samu kuri'u 281 da suka bashi nasara a kan babban abokin hamayyarsa, Umar Mohammed Bago, dan jam'iyyar APC, wnda ya samu kuri'u 76.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel