Rikicin gwamnati da masarauta: Kungiya ta nemi Ganduje ya cire masu yada masa labarai

Rikicin gwamnati da masarauta: Kungiya ta nemi Ganduje ya cire masu yada masa labarai

Wata kungiya mai zaman kanta a Kano, Renaissance Coalition ta shawarci gwamnatin Jihar ta kori sakataren yada labaran Gwamna Abdullahi Ganduje saboda yadda ya tafiyar da batun rikicin da ke tsakanin gwamnan da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kakakin kungiyar, Ibrahim A. Waiya ya yi wannan kirar ne yayin da ya ke mayar da martani kan wani jawabi da aka ce sakataren yada labarai na gwamnan Abba Anwar ya yi kan sulhun da Aliko Dangote da kungiyar gwamnonin Najeriya ke yi tsakanin shugabanin biyu.

Ana zargin sakataren yada labarai na gwamnatin da cewa ba a fara sulhu ba tsakanin sarki da gwamna wanda kungiyar na ganin hakan na da hatsari kuma barazana ce ga zaman lafiya a jihar.

DUBA WANNAN: Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

A cewar Waiya, "A matsayin mu na 'yan asalin Kano masu son zaman lafiya, muna mamakin yadda wasu ke kokarin ganin rikicin da ke tsakanin sarki da gwamnan Kano ta cigaba duk da cewa hakan na iya kawo tabarbarewar tsaro a Najeriya.

"Babban matsalar mu shine wasu da aka daura wa alhakin yin magana a madadin gwamnatin Kano da suka hada da Salihu Tanko Yakasai da Aminu Isah Abba Anwar cikin 'yan kwana kin nan suka nuna rashin kwarewa a cikin aikinsu yayin da suka yi ikirarin cewa ba a yi sulhu ba tsakanin gwamna da sarkin Kano.

"A halin yanzu Najeriya na fusakantar barazanar tabarbarewar tsaro saboda haka ba mu bukatar wasu mutane su rika yada maganganun da ka iya janyo rikici a Kano.

"Saboda haka muna bukatar gwamnan ya yi watsi da jawabin da su kayi kuma ya cire su daga matsayin su domin ba su cancanta ba," inji Waiya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel