Fara wa da zafi-zafi: Gbajabiamila ya nada Sanusi a matsayin shugaban ma'aikatansa

Fara wa da zafi-zafi: Gbajabiamila ya nada Sanusi a matsayin shugaban ma'aikatansa

Sabon zababben shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi nadin mukami na farko bayan 'yan mintuna kadan da samun nasarar zama shugaban majalisar wakilan Najeriya.

Gbajabiamila ya nada Sanusi Rikiji, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, a matsayin shugaban ma'aikatansa.

Sabon shugaban majalisar ya yi godiya ga tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, bisa rawar da ya taka wajen nasarar da ya samu.

Kafin ya lashe zaben kujerar shugaban majalisar wakilai a yau, Talata, 11 ga watan Yuni, Gbajabiamila ya kasance shugaban masu rinjaye a zauren majalisar tun shekarar 2015.

Gbajabiamila, zabin jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa, ya samu kuri'u 281 da suka bashi nasara a kan babban abokin hamayyarsa, Umar Mohammed Bago, dan jam'iyyar APC, wnda ya samu kuri'u 76.

Tun kafin a kammala kidayar kuri'u Bago ya mike tare da zuwa wurin Gbajabiamila domin taya shi murnar samun nasarar lashe zaben kujerar kakakin majalisar wakilai.

DUBA WANNAN: Abinda Sanata Ali Ndume ya fada wa APC bayan Sanata Ahmed Lawan ya kayar da shi

Kazalika, a majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, danlelen shugaban kasa da jam'iyyar APC a zaben shugaban majalisar dattijai, ya samu nasarar buga abokin hamayyarsa da jam'iyyar PDP ke mara wa baya, sanata Ali Ndume, da kasa a zaben da aka yi yau, Talata.

Lawan ya zama sabon shugaban majalisar dattijai bayan ya samu adadin kuri'u 79, yayin da abokin takararsa kuma shalelen jam'iyyar PDP, Sanata Ndume, ya samu kuri'u 28 kacal.

Sanatoci 107 da ke zauren majalisar dattijai ne suka kada kuri'un zaben wanda zai jagorance su. Majalisar na da jimillar mambobi 109 amma har yanzu hukumar zabe ba ta kammala warware matsalar Sanatoci biyu ba daga jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel