Bukatarmu kawai ita ce ka bayyana Abiola a matsayin shugaba kasa – NADECO ga Buhari

Bukatarmu kawai ita ce ka bayyana Abiola a matsayin shugaba kasa – NADECO ga Buhari

Rahotanni sun kawo cewa jiga-jigan kungiyar kare muradin siyasar Yarbawa kawai (NADECO), sun yi kira ga shuaban kasa Muhammadu Buhari kan ya bayyana sunan marigayi Cif MKO Abiola a matsayin shugaban kasa.

Sun kuma nemi da a kira babban taron makomar Najeriya domin kamo bakin zaren yadda Najeriya za ta ci gaba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Wadanda suka yi wannan kira, wadanda a cikin su har da tsohon gwamnan soja na Jihar Lagos, Ndubuisi Kanu, Amos Akingba da Ayo Opadokun, sun yi wannan kira ne a lokacin da suke ganawa da manema labarai a jihar Lagas.

Da ya ke karanta takardar bayanin nasu, Opadokun ya ce irin wannan taron zai kunshi shugabannin kabilu daban-daban na kasar ba wai wasu wakilai da gwamnati za ta nada su wakilci jama’a ba.

Sun ce maida komai dungurugun a hannun gwamnatin tarayya da aka yi, ya haifar da cikas a wurare da dama.

NADECO ta ce ta yi amanna ce wa komawa a kan dokar Najeriya ta 1960, wadda ta damka albarkatun karkashin kasa na kowane yanki a yankin da arzikin ya ke, ita ce mafita domin kawo ci gaban kowane yanki a kasar nan.

Daga nan NADECO ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanu da rikice-rikicen Fulani da makiyaya a fadin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa nayi takara da Omo-Agege - Ekweremadu

Kungiyarta kuma yi kira da a gaggauta bayyana sunan Marigayi Mashood Abiola a matsayin shugaban kasa, duk kuwa da cewa ya rigaya ya mutu tuni.

Ta kuma nemi a samu wani katafaren gini na gwamnatin tarayya a sa masa sunan Abiola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel