Sojoji sun gano shirin kungiyar ISWAP na daukan sabbin mayaka

Sojoji sun gano shirin kungiyar ISWAP na daukan sabbin mayaka

Dakarun tsaron hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) ta ce ta gano wani shiri da kungiyar ta'addanci ta Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ke yi na fara daukan sabbin mambobi cikin watanni masu zuwa ta hanyar yada da'awa ta karya da juya tunanin matasa.

Cikin sanarwar da kakakin MNJTF, Kwanel Timothy Antigha ya fitar, ya bukaci sarakunan gargajiya, shugabanin addinai, shugabanin al'umma da iyaye su sanya idanu kan yaransu domin kare su daga sharrin 'yan ta'addan.

Ya ce ISWAP na shirin fara labaran karya da farfaganda domin kada su rasa mambobin su da kuma yunkurin janyo hankalin sabbin mambobi.

DUBA WANNAN: Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

Antigha ya ce ISWAP ta soma yada farfaganda ne sakamakon kayen da suka sha hannun sojoji a makonnin da suka gabata.

Ya kara bayanin cewa 'yan ta'addan sun yi karya inda suka yi ikirarin kai hari a sansanin sojoji a Najeriya da Jamhuriyar Nijar cikin mujallar NABA na ranar 7 ga watan Yuni.

"Wadannan bayanan tsantsagwaron karya ne kuma muna kira ga mutane suyi watsi da shi.

"Zancen gaskiya ita ce ISWAP sun yi yunkurin kai hari a yankin Tafkin Chadi amma suka sha kashi hannun sojoji.

"Wannan ya sa suka koma wallafa labaran karya cikin mujallarsu ta farfaganda.

"Saboda abinda ke faruwa, yana da muhimmanci a gargadi mutane suyi takatsantsan da karerayin da ISWAP ke yadawa a yunkurin ta na samun sabbin mambobi.

"Abinda su ke nema shine su janyo hankalin matasa su shiga kungiyar domin maye gurbin wadanda MNJTF suka kashe karkashin Operation Yancin Tafki," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel