Za mu kunyata masu cin hanci ta hanyar bayyana sunayensu - Buhari

Za mu kunyata masu cin hanci ta hanyar bayyana sunayensu - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da sabbin dabarun yaki da rashawa a Najeriya inda ya ce za a bayyana sunayen dukkan wadanda aka samu da aikata rashawa domin a kunyatta su.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wurin taron yaki da rashawa da a kayi a Abuja domin bikin ranar Demokradiya.

Ya ce za mu fara amfani da tsarin yi wa masu rashawa tonon silili ta hanyar fitar da sunayensu kowa ya san su yayin da za mu karrama wadanda suka guji aikata rashawar.

DUBA WANNAN: Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

"Ina farin cikin sanar da ku cewa kwamitin bawa shugaban kasa shawara kan rashawa (PACAC) ta fara tattaunawa da sauran hukumomin yaki da rashawa domin cimma wannan burin," Inji Shugaban kasar.

Ya ce tattaunawar tsakanin PACAC da sauran hukumomin yaki da rashawa zai karfafawa Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomin yaki da rashawa gwarin gwiwa da gudun mawar da suka bukata wurin gudanar da ayyukansu.

Shugaban kasar ya ce za suyi hadin gwiwa da fannin shari'a wurin toshe dukkan gibin da masu aikata laifi ke amfani da su wurin aikata laifi.

Ya kuma ce za su tabbatar dukkan masu rike da mukaman gwamnati sun bayyana kadarorin su tare da tanadar da hukunci da lauyoyi, ma'aikatan banki, masu hada-hadar hannun jari da sauran wadanda ke taimakawa masu aikata rashawa.

"Za mu tabbatar da tsaro da tallafi ga wadanda ke yi wa masu rashawa tonon silili da kuma wadanda suka fada cikin fitina sakamakon rashawa," inji Shugaba Buhari.

Har wa yau, shugaban kasar ya ce za su fadakar da 'yan Najeriya da ke karkara su tsunduma cikin yaki da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel