Saurayin daya rataye budurwarsa ya fuskanci matsanancin hukuncin kisa daga Kotu

Saurayin daya rataye budurwarsa ya fuskanci matsanancin hukuncin kisa daga Kotu

Wata babbar kotun jahar Yobe ta yanke ma wani matashi Muhammad Adamu hukuncin kisa bayan ta kamashi da laifin kashe budurwarsa, Hauwa Muhammad, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotu, mai sharia A Jauro ya bayyana cewa ya kama Adamu da laifin hukuncin kisa a karkashin sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka.

KU KARANTA: APC ta tsayar da mutumin daya saci sandan majalisa a matsayin mataimakin shugaban majalisa

Jauro yace lauyan masu kara ya gamsar da kotu da gamsassun bayanai dake nuna cewa da gangan Adamu ya kashe Hauwa, don haka yace hukuncin kisa ta hanyar rataya ya haushi kamar yadda sashi na 273 na kundin hukunta manyan laifuka ta tanada.

“Da wannan dalilin na yanke maka kai Muhammadu Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya, da fatan Allah ya yi maka rahama.” Inji Alkali Jauro.

Da yake ganawa da manema labaru, lauyan mai kare Adamu, M Dauda ya bayyana cewa zai je ya karanci hukuncin kotu tare da yin zuzzurfan nazari game da hukuncin domin duba yiwuwar daukaka kara.

Shima Adamu wanda aka yanke ma hukuncin kisan ya bayyana cewa ya dade yana addu’ar Allah Yasa a yanke masa hukuncin da yafi alheri “Na yarda da ikon Allah, na yarda haka Allah Ya nufeni da wannan hukunci, kuma na rungumi hukuncin.”

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar Yansandan jahar Yobe ce ta shigar da karar Adamu a ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2018 bayan ta samu rahoton ya kashe budurwarsa a ranar 29 ga watan Mayu na 2018 sakamakon cacar baki data kaure a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel