Gaskiyar dalilin da yasa nayi takara da Omo-Agege - Ekweremadu

Gaskiyar dalilin da yasa nayi takara da Omo-Agege - Ekweremadu

Sanata Ike Ekweremadu (PDP Enugu) a ranar Talata, 11 ga watan Yuni ya bayyana ainahin dalilin da yasa shi takarar kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa a lokacin rantsar da majalisar dattawa ta tara a Abuja.

Ekweremadu wanda ke wakiltan Enugu ta yamma, ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaben a harabar majalisar dokokin tarayya.

Legit.ng ta rahoto cewa Ekweremadu wanda ya kasance tsohon mataimakin Shugaban majalisar wakilai tare da Sanata Ovie Omo-Agege ne suka yi takarar neman kujerar.

Yayinda Ekweremadu ya samu kuri’u 37 cikin105, Omo-Agege ya samu kuri’ u 68 inda ya zama sabo mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

Yace a yanke shawarar takara ne domin yin zanga-zaga akan tsayar da Omo-Agege a matsayin wanda ake son ya dare kujerar mutum na biyu a majalisar dokokin tarayya na tara.

Ekweremadu ya bayyana cewa babban abin kunya ne a tarihin Majalisar Dattawan Najeriya a ce gogarman da ya shirya harkallar sace Sandar Mulkin Majalisa ne aka zaba Mataimakin Shugaban ita majalisar.

K KARANTA KUMA: Yadda zaben kakakin majalisar wakilai ke gudana

Ya kara da cewa, dama bai yi tunanin zai yi nasara ba, amma dai ya fito ne saboda cin fuskar da aka yi wa majalisa a karkashin jagorancin Sanata Ovie Omo-Agege.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel