Zaben Majalisa: Kamata ya yi jam'iyyar APC ta yi min jinjina - Sanata Ndume

Zaben Majalisa: Kamata ya yi jam'iyyar APC ta yi min jinjina - Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume, dan takarar neman kujerar shugaban majalisar dattijai da ya sha kaye, ya ce kamata ya yi jam'iyyar APC ta yaba masa saboda takarar da ya yi da Sanata Ahmed Lawan, shalelen shugaba Buhari da jam'iyyar APC.

Ndume ya ki janye takararsa duk da jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa sun fito fili sun bayyana goyon bayansu ga Lawan.

A zaben da aka gudanar a ranar Talata, Ndume ya samu kuri'u 28, yayin da Lawan ya samu kuri'u 79.

Da yake magana jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben, Ndume ya ce mutuncin jam'iyyar APC zai shiga tsaka mai wuya da a ce bai yi takara da Lawan ba.

"Babu dimokardiyya a duk inda babu 'yan takara. Hakan ne yasa na tsaya tsayin daka a kan takara ta. Sashe na 50 (1) na kundin tsarin mulki ya bawa Sanatoci damar zaben shugaban majalisar dattijai da mataimakinsa, kuma hakan ce ta faru a zauren majalisar," a cewar Ndume.

DUBA WANNAN: Yakubu Danladi, wani matashi mai shekaru 34, ya zama kakakin majalisar dokoki a jihar Arewa

Sannan ya cigaba da cewa: "kuri'u 28 na samu, hakan shine dimokradiyya kuma na yarda cewar an gudanar da zabe sahihi na gaskiya da babu wani boye-boye a cikinsa.

"Ni ne na dage a kan yin zabe cikin sirri amma a bainar jama'a, yin hakan ya kara wa zaben kima da mutunci.

"Da a ce na yi biyayya ga umarnin jam'iyyar APC na goyon bayan Lawan a matsayin dan takara daya tilo da zai nemi kujerar shuganci majalisar dattijai, da na tabbata sai hakan ya taba kimar jam'iyyar da gwamnatin tarayya. Shi yasa bana ganin kai na a matsayin maras nasara. Na samu nasara kuma ya kamata jam'iyya ta yaba min."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel