Majalisa: Ikpeazu da Gbillah sun amince da takarar Gbajabiamilla da Bago

Majalisa: Ikpeazu da Gbillah sun amince da takarar Gbajabiamilla da Bago

A daidai lokacin da ake shirin gwabzawa tsakanin manyan ‘yan takarar da ke neman kujerun majalisar tarayya, sai aka ji labari cewa wasu ‘Ya ‘yan PDP sun sabawa umarnin uwar jam’iyya.

Wata ‘yar majalisa daga yankin jihar Anambra da ke jam’iyyar PDP ce ta goyi bayan tsaida Hon. Femi Gbajabiamilla da aka yi a matsayin ‘dan takarar shugaban majalisar wakilai na tarayya

Abdulmumin Jibrin shi ne ya tsaida Honarabul Femi Gbajabiamilla a matsayin ‘dan takara a zaben bana. Nan-take Linda Ikpeazu ta PDP tayi caraf, ta tashi, ta na mai na’am da wannan zabi.

Honarabul Linda Ikpeazu ta na cikin ‘yan majalisar da ke tare da jam’iyyar hamayya, amma ta nuna goyon bayan ta ga ‘dan takarar da jam’iyyar APC mai mulki su ke marawa baya a zaben.

KU KARANTA: Yadda Ahmad Lawan ya yi ta fadi-tashi domin ya gaji Bukola Saraki

Wannan mataki da Linda Ikpeazu ta dauka, ya zama akasin matsayar da jam’iyyar PDP ta cin ma a Ranar Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019. PDP ta nuna cewa tana tare ne da Honarabul Umar Bago.

Haka zalika wani ‘dan majalisar APC daga jihar Gombe, Abubakar Ahmad, ya daga hannun Hon. Umar Bago a matsayin ‘dan takararsa, wanda Mark Gbillah na jam’iyyar PDP ya nuna goyon baya.

Idan ba ku manta ba, PDP ta fito ta nuna cewa za ta marawa Sanata Ali Ndume da kuma Hon. Umar Bago baya ne a zaben majalisa ta tara, akasin zabin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel